Advertisment
News

Makwabcin Nane Ya Sacemin ‘Yata Ya Kasheta Bayan Ya Karbi Naira Miliyan 8 Awajena

Sponsored Links
Al umma na zuwa jaje gidan Alhaji shua aibu wa alamu wambam dawaki
Wanda shine mahaifin yarinyar da aka sace Mai shekaru 8 da haihuwa ana Kuma zargin makwabcinsa da hada Baki da masu garkuwa da mutane wajen sace yarinyar da karban kudin fansa naira miliyan takwas a matsayin kudin fansa

{wannan itace asma’u din da aka sace Kuma aka Kasheta}

Lamarin dai ya faru ne a cikin birnin Zaria take jihar kaduna state
Ana dai zargin makwabcin wa alamu da kisan yarinyar Mai suna asma’u  bayan ya hada Baki da masu garkuwa da mutane
Inda suka Kasheta bayan sun karbi kudin fansa nata
[wannan shine mahaifin asma’u]
Mahaifin asma’u yace tun ranar 9 ga watan December 2021 aka sace Yar tasa tun lokacin Kuma suka sanar da Yan sanda tare da Kai cikiyar ta wurare da dama
Sai dai daga baya an Fara Kiran lambar wayar sa
Inda aka bukaci ya bayar da kudin fansar Yar sa naira miliyan 15
Ya Kara dacewa daga baya mun Basu naira miliyan 2
Bayan mun Kai musu kudin unguwar rigasa dake kaduna sai sukace sai mun Kara musu da naira miliyan 1 da naira dubu 45 kafin su sakomin Yar tawa
Bayan mun biyasu kudin da suka bukata sai Suka kirani ranar 19 ga watan January Suka cemin sun kashe min Yar tawa suna Gama fada suka kashe wayar su Basu sake kirana ba
Alhaji shua aibu wa alamu yace tin kafin su Gama biyan kudin sun gano Wanda ya sace musu Yar su kawai suna bin Umarnin sune saboda Kar su kashe Masa Yar sa
Amma duk da hakan ma sai da suka kashe Masa yarinyar sa
Mahaifin yarinyar yace sun tabbatar da hakan ne saboda kwararar hujjoji da suke da su cewa makwabcin sune ya sace musu Yar su
Zuwa yanzu sai jami an Yan sanda masu yaki da muggan laifuka na IRT sun Kama Wanda ake zargin domin fadada bincike
Allah ya Kara tsare mu daga maciya Amana
Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button