Job

Sabuwar Dama Yadda zaku Nemi aiki a OPAY

Yadda zaku nemi aiki a OPAY matsayin state sector manager.

Yadda zaku cike wannan aikin na OPAY matsayin state sector manager, wannan bankin na OPAY Yana da cikkyakyan lasisi da babban bankin Nageriya wato central bank of Nigeria (CBN).
Wannan bankin an kaddamar dashi ne a shekara ta dubu biyu da Sha takwas wato 2018 Wanda suna da hedikwata a dukkan sassan fadin kasar Nageriya wato dukkan jahohin Nageriya guda talatin da shida 36 states sannan suna da manyan kwastomomi akalla guda 300,000 Wanda suke hada Hadar kasuwanci da wannan bankin na OPAY.
Sun tsara wannan bankin na OPAY domin bawa kowa damar yin kasuwanci dasu domin suna da cikkyakyan lasisi da Kuma tsaro da tsari me kyau.
Wannnan bankin na OPAY ya kasance babban kamfani na hada Hadar kasuwanci musamman ta bankaren POS domin fidda kudi ko musayar kudi da makamantan su.
A tare da wannan bankin na OPAY zaku iya tura kudi, siyan katin lantarki, biyan kudi ta online wato ta hanyar Remita, siyan katin waya, siyan Abu ya online, bukin na Visa domin tafia Wata kasa da sauran makamantan su.

Wannan aikin na OPAY an Masa take da sunan state sector manager (sales).
Wanda ya shafi aikin kula da taimakawa wannan bankin ta hanyar bunkasa muradin kwastomomi da bunkasa kudin shigowar wannan bankin Wanda hakan zai taimaka Wajen samun cigaban wannan bankin.
Ga dukkan Wanda ya samu wannnan aikin na OPAY dole ne akwai wasu ayyukan da zai kasance Yana kula da su kamar haka.

  1. Kawo cigaba tare da shirya gudanar da kasuwanci Wanda zai Kai ga samun nasara.
  2. Shirya fannin kasuwanci tare da tsare yadda za’a samu Karin kwastomomi da Kuma kiyayewa muradin su.
  3. Gina babbar alaka tsakanin masu saka jari a wannan bankin na OPAY.
  4. Bayyana yadda tsarin shige da fitar kudi ya kasance tare da hasahen na gaba ga shugan wannan bankin na OPAY.
  5. Bayyana yadda manufar kasuwanci kamfani zai gudana tare da kawo sabbin abubuwan cigaba.

Abinda ake nema Wajen daukan wannan aikin na OPAY sun hada kamar haka:-

Dole me cikewa ya kasance Yana da digiri ko master a bangaren business administration.

Ko Wanda ya kasance yayi aiki a matsayin pharmaceutical manager.

Dole ne ya kasance Yana da gogewa a bangaren kasuwanci ko na Wata ma’aikata da yayi aiki a cikinta.

Sannan dole ne ya samu gogewar ta wanni fanni aiki da yayi na akalla tsawon shekara 3 zuwa 5.
Domin cikawa danna wannan shudin rubutun dake kasa
👇👇👇👇

APPLY NOW


Shiga WhatsApp group namu da Facebook page, Danna wannan shudin rubutun dake kasa.
👇👇👇👇👇

Whatsapp group 1 Facebook page

whatsapp group 2

Ziyarchi Shafukanmu Na WhatsApp group 1, WhatsApp group 2, WhatsApp group 3, Facebook page, da Telegram.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button