Advertisment
News

Sanarwa Ga Dukkan Wanda Suka Nemi RRR wato Tallafin kudi na NASSCO

Sponsored Links

Sanarwa ga dukkan Wanda suka nemi RRR wato tallafin kudi na NASSCO.

Shin Minene Shirin RRR? Shirine Wanda Gwabnatin tarayya ta Nigeriya ta fitar Wanda zata taimaka matasa da masu karamin karfi da tallafin kudi na kimanin naira dubu biyar tsawon kimanin Wata 6, Da farko an turawa wasu a watan farko wasu Kuma ba’a tura musu ba Sai daga baya sannan aka turawa mutane da dama Wanda aka hada musu duk na watanni Shida ahade yazana sun samu kimanin kudi naira dubu talatin #30,000. Amma akwai Wanda har yanxu ba’a tura musu duk da cewa tun farkon cikewa sukayi Amma shiru domin kuwa Ana turawa ne kadan kadan domin haka kada KU damu naku Yana Nan zuwa.

Bayan an cike na farko to daga baya ma an Kara fiddawa inda mutane da dama suka samu cika cike Wanda cikawa bashi da wuya saboda nayin dialing ne da number waya.
Babban abin da yake faruwa yanxu shine ga dukkan Wanda ya cike na a karona biyu to anfara bi unguwanni Ana karban bayanan mutane domin a aika sunan su zuwa Abuja saboda haka inde kasan ka cike wannan tallafi na RRR ko wani Dan uwanka ya cike ka sanar dashi akan Ana zuwa unguwanni Ana bayar da suna da account number sannan Ana daukar hoton Wanda ya cike da sauran abubuwa.
Idan har kasan ka cike to kayi kokarin bincika Mike gudana a unguwar da kake saboda mutane da dama sun cike Amma Basu je sun bayar da bayanan su ba kaga anyi asara kenan, da farko suna Kiran mutane su sanar dasu inda zasuje a tura bayanan su saide kamar yanxu abin ya musu yawa dole ne Wanda ya cike ya neme su da Kansa saboda kada agama bai sani ba.
Ga daga cikin abubuwan da yakamata kaje dasu Wajen da za’a tura bayanan ka.
Ka tabbatar kaje da abubuwa kamar haka:-

Takadar shedar Dan kasa wato NIN ID CARD.

Katin haihuwa Wanda ka cike BVN naka da shi.

Number ka ta banki wato account number.

Number ka ta BVN.

Sannan da number wayar ka.

Domin Karin bayani Shiga WhatsApp group namu

WHATSAPP GROUP

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button