support

WASU DAGA CIKIN DOKOKI DA KUMA TSARE-TSARAN DA GOOGLE SUKE SO MUTUM YA BI KAFIN SU KARBI SITE KO CHANNEL NASA

*WASU DAGA CIKIN DOKOKI DA KUMA TSARE-TSARAN DA GOOGLE SUKE SO MUTUM YA BI KAFIN SU KARBI SITE KO CHANNEL NASA*  
👂🏻 Ka da ku manta na ce wasu daga ciki.
_Mafi akasarin mutanamu_ mun shiga harka Google Earn ba tare da da duba tsare-tsare da kuma dokokinsu ba. Wani lokacin sai ka ga mutum yana ta applying for many times amma sai ka ga sun ki karbar site ko channel din. Hakan na faruwa ne saboda rashin bin ka’idojinsu da kuma dokokinsu.
🤣 Even ni da nake wannan maganar, sai da na yi applied suka dawo da ni, sannan na je da duba wadannan dokoki da tsare-tsare.
Mutane sukan ce akwai hawa Lucky a harkar, eh nima zan iya yarda da hakan amma wallahi mutanan nan idan har ka bi dokarsu approve kamar an yi ma ne.
Wasu daga cikin dokokin sun hada da;
⚠️ Ba sa san abun da zai haifar da kiyayyar, wariya, cin mutumcin mutum musamman ma a ce sananne ne, kushe wata kungiya ta addini ko kabila, ko wasu abubuwa da suka danganci sex.
⚠️ Ba sa san daukar wani abu da ba naka ba, wato ba sa bukatar halin maciji🤣🤣
⚠️ Ba sa san labari na abun da ya danganci tashin hankali, yaki d.s.s ko kuma ba da labari na abun da ya danganci cin zarafi. Misali; yadda aka yi wa wani walakanci aka kore shi.
⚠️ Ba sa san ba da shawara ko koyar da wani abu da idan aka yi amfani da shi zai cutar da lafiya ko hankali; kamar kayan maye d.s.s
⚠️ Ba da labari kan yadda wani ya kashe kansa, ko kuma koyar da hakan.
⚠️ Abun da ya danganci  ta’addanci ko safarar mukamai
⚠️ Koyar da yadda za a zalunci dabbobi kawai dan nishadi; kamar kare ko dabbobin jeji
⚠️ Koyar da yadda za a saci bayanan sirri na wani ko wata ma’aikata.
⚠️Koyar da yadda ake kirkirar takardun karya; kamar certificate ko passport. Da kuma koyar da duk wata hanya da za a cuci ko a yaudari jama’a ko wata ma’aikata
⚠️ Koyar da yadda ake hacking ko kuma samarwa mutane wasu abubuwa (apps) da za su ba da damar shiga wata kafa ba da izini ba.
⚠️ Koyar da trekking ko samar da wasu hanyoyi waɗanda ke bawa mai amfani damar yin leke ko saka idanu akan wani mutum ko ayyukansu ba tare da izininsu ba.
⚠️ Koyar da yadda za ayi amfani da software ko “malware” wanda za su iya cutarwa ko samun dama ga computer ko wata  na’ura ta hanyar sadarwa mara izini.
⚠️ Koyar da abubuwan da suka danganci sex; ko da kuwa ba a ambaci kalmar sex din ba. Misali yin amfani da wasu bakin kalmomi wayan kayar da yadda ake karuwanci d.s.s.
*Note*👂🏻
Kamar yadda kuka sani dokokin nasu da yawa, wadannan wasu daga ciki na kawo base on my understanding.
Sannan kuma idan suka yi approved naka zaka iya cigaba da lankwasa wasu daga cikin dokokin.
Misali, wadanda suke harkar news, a dokarsu ba sa san labarin da ya danganci ta’addanci, kyamar wani d.s.s kuma gashi labaran kasar tamu duk sun kunshi hakan. Idan sun yi approved za ka iya dawowa ka cigaba, saboda kasan lokacin da aka yi apply sun fi bin kwakkwafi.
Haka su ma masu harkar tech; basa san trekking, koyar da yaudara ko wata dabara da za a yi abu ba bisa ka’ida ba. dss. Idan sun yi approved za ka iya dawowa da wasu, amma ko kadan ka yi amfani da kalmar *hacking* ko *trekking* kana ruwa🤣🧖‍♂️
Allah ya sa mu dace Ya kuma kara hada kanmu baki daya.
✍️ M.SHÈÈTÛ

Ziyarchi Shafukanmu Na WhatsApp group 1, WhatsApp group 2, WhatsApp group 3, Facebook page, da Telegram.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button