Advertisment
News

YAN ADAIDAITA SAHU SUN JANYE YAJIN AIKIN DA SUKEYI A JIHAR KANO

Sponsored Links
Ƙungiyar masu tuƙa baburan A-Daidaita-Sahu a Jihar Kano ta janye yajin aikin da take yi,
Barrista Abba Hikima wanda shi ne lauyan da ke kare ƙungiyar ne ya sanar wa manema labarai da matakin da ƙungiyar ta ɗauka na janye yajin aikin.
Tun a ranar Litinin, 10 ga watan Janairun 2022 aka wayi gari da yajin aikin direbobin A-Daidaita-Sahu.
An soma wannan yajin aikin bayan masu A-Daidaita-Sahun sun yi zargin cewa ana karbar musu kudade na yin sabuwar lambar da suka yi rijista maimakon biyan kudin sabuntawa.
Kazalika, sun ce ana tatsar su sosai wajen karbar haraji daga naira 100 da suka saba biya yanzu an mayar naira 120 a kowace rana.
Sannan a cewarsu, sun nemi gwamnati ta dauke musu biyan harajin ranakun Lahadi tun da jami’an hukumar Karota ba sa fita aiki a ranar.
Sai dai gwamnatin Kanon ta ce masu A-Daidaita-Sahun ba su da godiyar Allah.
Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button