Advertisment
Tech & Guide

Yadda Zaka Kare Facebook Account Dinka Daga Sharrin Hackers

Sponsored Links

HANYOYIN DA HACKERS SUKE BI DOMIN SHIGA
CIKIN SHAFUKAN JAMA’A MUSAMMAN
FACEBOOK
*
*
*
*
*
*
*
*
*
Kamar yanda na dauki alkawari ma wasu daga
cikin abokai na masu muhimmanci cewa idan
nasamu dama zan danyi karin haske akan
wadannan matsalolin dasuka addabemu
ashafukan yanar gizo musamman yankinmu na
arewa awannan shekarar abin har yayi matukar
muni,
yayinda kwatsam ake shiga Facebook din mutane
ana sauya musu suna babu gaira babu dalili.
wasu kam abin har yakaiga hallakar account
dinsu.
koma dai menene duk munsani abin baiyi mana
dadi ba, muna ganin yadace ace mun dauki
mataki akai.
yanada kyau ka juri karanta wannnan rubutun
sannan kadauketa da muhimmanci.
idan kasani akwaii wadanda basu sanu ba
dafarko dai zan zanyi magana akan Hacking.
anawa fahimtar ana nufin kutsa kai cikin wani
abu ta barauniya
hanya batareda sanin ma malllakin ita wannan
abin ba.
idan kuma muka duba hacking na facebook shine
kutsa kai cikin shafin wani batareda izininsa ba.
wato abinda yazama ruwan dare awannan
zamani da muke ciki kenan.
daga cikin dalilan dasuke sa ayi hacking akwai
mallakar abu mai muhimmanci wanda yake
dauke hankalin dan kutsen har yakwadaitu da
zuwa yakwata koda kuwa da karfin tsiya ne.
shin menene daliln dayasa mu yan arewa akafi
kwace mana shafukan facebook tareda lalata
mana su.
na farko akwai sakaci dakuma ganganci wanda
hakan shike bawa masu kutse daman 80% su
shiga su aikata mana ta’adi yanda sukeso.
sakaci da kuma gangancinmu anan shine rashin
sanin muhimmancin password ko kuma ince
rashin ingantashi misali mutum ne zaka samu
yana amfani da lambar wayarshi amatsayin
password dinshi.
ko kuma kayi amfani da wani bangare na lambar
ka amatsayin password.
bari inbada wani misali agaskiya idan. wannan
misali tashafeka
sai kayi kokarin gyarawa.
misali.
mukaddara inaso zan kutsa cikin account dinka
domin in aikata maka wani ta’adi da farko
zanfara jarrabawa ne da lambarka tahanyar
hasashe wato prediction aturance ko kuma
ince guessing.
Mukaddara kabada damar ganin lambarka a
profile dinka nashiga sai nayo copy ace lambarka
itace wannan 09035668852 sai inje wurin login
insaka lambarka tahanyar pasting tunda dama
can nayo copy dinta wurin saka password sai
inkuma saka lambarka din.
idan nasamu damar shiga toh fa shikenan idan
kuma password dinka ba haka bane sai in cire
090 nafarko insaka da 35668852 insake komawa
password dinka ingwada idan hakanma bata
yiwuba sai in sake cire lambobi uku na karshe
wato insaka daga 09035668 sai ingwada idan
hakane madallah idan bahaka bane sai in dubi
sunanka sai ingwada amatsayin password misali
RILWAN da manyan harufa idan baiyiba sai
ingwada da kananan harufa idan hakanma
baiyiba sai inkuma dauko karshen lambarka
insaka akarshen sunanka misali RILWAN52
zangwada da kananan harufa ma haka.
idan baiyi ba hakanma sai in bincika ya yanayin
ka yake shin kana yin soyayya ne? ko kanada
aure?
idan amsar eh ne toh shin me sunan budurwarka
ko matarka? zanyi kokari ingano duk sabida
kawai insamu damar shiga indebi bayanan
danake bukata aciki. haka Zanyi ta hasashe har
sai na gano kalmar sirrinka, karkaji lokacinda yan
kutse ke kashewa domin lalata abinda suka
sanya agaba idan har baka tsira daga matakan
dana
irga dinnan ba tofa yanada kyau kayi kokari
kasauya password dinka tahanyar saka symbols
aciki da kuma garwaya harufa manyan da
kananan lambarka kuwa kaboyeta daga cikin
profile dinka,
idan kayi nasarar magance wadannan toh fa sai
dai dan
kutse yabi wasu hanyoyin dazanyi bayaninsu
badai yayi hasashe ba.
2 forget password
Suna iya shiga Facebook dinka tahanyar forget
password.
kamar yanda nayi bayani suna iya hasashen gano
password na Facebook haka simple suke gano na
email atafiyar da muke ciki har anfi amfani da
lamba amatsayin password na email fiyeda
facebook abin har yazama jiki tayanda akasari
wadanda aka bude musu email a cafe zaka samu
lambarsu ne password dinsu. kaga hakan zai
bawa dan kutse damar shiga account dinka cikin
sauki koda kuwa password dinka yanada wahalar
ganewa idan yayi forget password shikenan koda
kana
aiki da approval pin ne.
haka yakan iya yin amfani da wani software da
ake kira spy Phone.
spy phone wata software ce datake bada damar
ganin duk wani abinda ake aikatawa a wayarka
dazarar takasance awayarka takan iya daukan
record din maluhallinka da kuma na kiran dakayi,
sakonnin dasuke shigowa wayarka, irin apps din
dakake amfani dasu awayarka da sauransu tana
tura bayanan zuwa gareshi dan kutsen dayasaka
ma ita wannan software din.
kaga idan yayi forgot password zasu tura maka
confirmation code tayanda dazarar yashiga cikin
spy software dinsa zata nuna masa, sai
yadauketa yaje yashiga account dinka yayi duk
abinda yaga dama.
idan kanason kagane wayarka akwai spy
software ko babu sai kaje settings kashiga apps
daga nan sai kashiga running services duk wani
abinda ba kasan dashi ba sai kayi uninstall dinsa
cikin sauki.
ka kuma nemi anti virus dazai rika kula da duk
abinda zai shigo cikin wayarka.
3 Phishing
phishin hanya ne mafi shahara da yan kutse suke
bi domin samun nasarar kutsawa cikin account
din duk wanda suke bukata.
taya ake phishing?
amsa itace zasu Gina shafi ne mai matukar
kama da facebook daga bisani su tura ma wanda
sukeson shiga account din nasa link din ita
wannan website din da suka ginan tayanda
dazarar kashiga zai kalleta tamkar Facebook
shafin haka zalika zaiga kamar kayi logout na
Facebook dinsa ne domin kuwa zaiga sun bukaci
kayi login na Facebook account dinsa ne awajen
dazarar kayi login details na account dinka zasu
kasance automatically text file kuma sukan iya
tsarata zata aika mai details dinka ta email
tayanda dazarar sunyi download dinsa shikenan
sunyi nasarar samun details dinka kuma hakan
zai basu daman shiga Facebook dinka .
yanda zaka magance kanka daga sharrin
phishing.
na farko shine ka kauracewa duk wani sako dazai
shigo email dinka ya bukaci kayi login na
Facebook dinka.

 • ba saita email kadaiba haka kwatsam kana iya
  cin karo dashi makamantan link wanda zaka
  gansu kamar facebook idan bazaka iya tantance
  wa ba yanada kyau karika amfani da chrome
  wajen shiga shafukan yanar gizo sabida ita
  chrome tana tantance phishing site tayanda
  dazarar zaka shiga zata nuna ma.
  4 keylogger
  keylogger aduk inda kaji ambaci keylogger wato
  wata manhaja ce da yan kutse suke kirkira su
  sanya ta acikin na’urar wanda suke bukata yima
  hacking din, tahanyar install dinta akan nau’rar
  tayanda zata rinka daukan duk wani abinda ake
  aikatawa acomputer din daga bisani ta aika
  musu bayanan data dauka din adunkule, ta
  hanyar email ko kuma FTP wato file transfer
  protocol.
  yanda zaka magance kanka daga sharrin
  keylogger.
  Nafarko shine kayi install na firewall software
  wanda zata baka damar tantance duk wani
  abinda zai shigo cikin na’urar ka kama daga
  online harma offline, aduk sanda wata manhaja
  ta waya kota computer ke kokarin fitarda
  bayanan sirri ita wannan firewall software din
  zata nemi izninka kafin abin yatafi kaga kenan
  hakan zai baka damar ganin duk wani abinda zai
  fita daga na’urar ka.
  -anti virus mai matukar inganci kuma yakasance
  updated one wato sabontacce.
 • ba kowanne sakone zaka kallesu ta email
  kabude su harma kayi download dinsu ba, hakan
  ma yana iya bawa dan kutse damar satar
  muhimman bayananka yayi awon gaba dasu.
 • yakasance kana sauya password dinka lokaci
  zuwa lokaci.
  akwai hanyoyin dayawa wadanda zama daya
  bazasu lissafu ba sabida haka zan dakata anan
  idan akwai me tambaya gameda abinda nayi
  magana akai zai iya yi….

RILWAN REALLY 09035668852

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button