Advertisment
News

Gobara Ta Lakume Kasuwar Nguru a Jihar Yobe

Sponsored Links

Labarin da yake fitowa yanzu daga Nguru, Jihar Yobe, yana cewa kasuwar garin Nguru ta tsinci kanta cikin iftila’in gobara a safiyar yau. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 8 na safiyar yau Asabar.

Gobarar ta fara ne daga bangaren masu sayar da takalma da robobi, kuma kawo yanzu ta lakume shaguwa da yawa. Tuni dai jami’an kai dauki da na kashe gobara suka isa wajen domin kai taimakon kashe gobarar. Matasan gari, jami’an ‘yan sanda, da sauran mazauna garin duk suna wajen domin taimakawa wajen kashe gobarar da kuma tabbatar da tsaro.

Allah ya kiyaye gaba, kuma Allah ya mayar musu da alkhairi.

Also Read: Yadda Taron Addu’a Don Kasa Ya Kasance: Hotunan Wajen Taron Addu’ar Zaman Lafiya

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button