Advertisment
News

Menene Gaskiyar Magana Akan Sabon Tallafi Da Ake Cewa Atiku Da Tinubu Zasu Bayar ???

Sponsored Links

Menene gaskiyar Magana Akan wasu shafuka ko nace link da ake yawan turawa mutane shi ta WhatsApp ko nace a kafar sada zumunta ta wacce ake Kira social media

Daga lokacin da aka kammala zaben fitar da gwani na jam’iyun siyasa ake samun wasu link da ake ta turawa mutane da sunan tallafi ne da Dan takarar shugaban kasa na jam’iyar Apc or pdp zasu bayar

Mutane da yawa suna Shiga wannan link din domin su cika wannan tallafin Amma sai su rasa ya Za’a su cika har suna Mana tambaya akai ma
To maganar gaskiya wannan link din ko nace shafukan Nan da kuke gani ba shafin cika tallafi bane suna yaudarar jama’a ne domin su Shiga shafin nasu Amma ba wani shafin tallafi na komai da wani Dan jam’iyar siyasa da ya bude a yanzu domin tallafawa Al’umma
A saboda Haka muke Kara Sanarwar da mutane su guji Shiga irin wannan shafukan
Saboda Za’a iya karban details naku a cutar da ku
Ta hanyar diba Muku kudi account or aje acika wani Abu Wanda dokar kasa Bata yarda da wannan abinba

Fatan kun fahimci bayanan mu Kuma Za’a kiyaye
Allah ya Kara tsare mu daga Sharrin Yan damfara da azzaluman bayi macuta ku cigaba da kasancewa da shafin ginsau domin samun ingantattun bayanai

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button